Isa ga babban shafi
Najeriya

Cin hanci ne ya sa aka yi min juyin mulki- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar aniyarsa ta yaki da cin hanci da rashawa tsakanin manyan hafsoshin sojin kasar ce, ta sa aka yi masa juyin mulki shekaru 31 da suka gabata. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

A wata hira da ya yi da mujallar The Interview, shugaba Buhari ya bayyana cewar tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da Janar Aliyu Gusau suka kifar da gwamnatinsa a shekarar ta 1985 don kare kansu daga tuhumar cin hanci da rashawa.

Buhari ya ce ya samu labarin cewar Janar Aliyu Gusau ya karbi lasisin shigar da kaya kasar wanda ya bai wa Alhaji Mai Deribe akan kudi Naira 100,000, abinda ya sa ya tuhume shi, ya kuma gabatar da zargin ga majalisar koli ta soja don hukunta Janar Gusau.

Buhari ya ce wannan ne ya sa aka kifar da gwamnatinsa don kare wadanda ake zargi daga tuhuma.

A watan Disambar da ta gabata, Janar Ibrahim Babangida ya yi hira da mujallar The Interview inda ya ce, babu alamun gaskiya kan zargin gabatar da tuhumar Janar Gusau ga majalisar soji.

Janar Babangida dai shi ne shugaban rundunar sojin kasa a karkashin mulkin Janar Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.