Masana Na Fargaban Za'a Fuskanci Yunwa a Arewa maso Gabashin Najeriya
Ayarin masana dake sa idamu a kan rikicin da ake yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa akwai alamun za'ayi fama da fari a yankin saboda kazamin ta'adi da ‘yan kungiyar Boko Haram suka janyo wa yankin.
Wallafawa ranar:
Ayarin masanan dake zaune a Amurka, karkashin suna 'Famine Early Warning Systems Network' sun fadi a wata sanarwa cewa mutane sama da miliyan uku na cikin wani hali a yankin kuma su na bukatar taimako.
Kungiyoyi irin wannan kan ayyana za’a sami fari muddin suka lura cewa kashi 20% na yankin da ake zance na fama da matsalar rashin abinci, ga matsanancin matsalolin rashin lafiya da sauran matsalolin rayuwa.
Dubban rayukan jama'a ne dai suka salwanta a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sakamakon hare-hare na 'yan kungiyar Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu