Isa ga babban shafi
Boko Haram

Boko Haram: Yara 50,000 na iya mutuwa saboda Yunwa a bana

An bukaci gwamnatin Najeriya ta kara daukar matakan magance matsalar karancin abinci tsakanin dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin arewa maso gabashin kasar.

Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya
Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya STRINGER / AFP
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara kanana kimanin 50,000 za su iya mutuwa a bana idan har ba gaggauta daukar matakan wadata su da abinci ba.

Kungiyar likitocin Doctors Without Borders tace akalla mutane 188 suka mutu tsakanin 23 ga watan Mayu zuwa 22 ga Yuni, sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Akwai tawagar gwamnati da ta kai ziyara sansanin ‘Yan gudun hijira a Bama domin ganin irin halin da ‘yan gudun hijira suke ciki, kafin bayar da tallafi daga gwamnatin Tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.