Isa ga babban shafi
Najeriya

Ekiti ta haramtawa Fulani kiwon shanu

Gwamnan Ekiti a Nigeria Ayo Fayose ya haramtawa fulani kiwon shanunsu a jahar a yayin da ake kokarin samar da mafita a rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar wanda ya janyo asarar rayukan mutane da dama.

Fulani makiyaya a Najeriya
Fulani makiyaya a Najeriya screammie.com
Talla

Mista Fayose ya bukaci alummar jihar da su kashe dukkan shanun da suka gani na kiwo a kowane sashe na jihar, sannan duk wani makiyayi da ya takale su shima su aika dashi lahira kamar yadda jaridun kasar da dama suka ruwaito.

Gwamnan ya furta kalaman ne a yayin da ya ziyarci alummar kauyen Oke Ako inda ake zargin makiyaya Fulani da hannu wajen kisan wasu mutane 2, a karshen makon jiya.

A cewar Gwamnan zai kuma aika wani kudirin doka zuwa Majalisar Dokokin jihar domin rattaba hannu don ganin an hana kiwon shanu a fadin jihar ta Ekiti.

Rikici tsakanin makiyaya Fulani da manoma a wasu jihohin Najeriya ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama inda ake yawan zargin Fulanin da hannu a kashe kashen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.