Isa ga babban shafi
Najeriya

Ohanaeze ta ba Fulani wa’adin kwanaki uku su fice yankin Igbo

Matasan kabilar Igbo karkashin kungiyar Ohanaeze ta ba al’ummar Fulani makiyaya wa’adin kwanaki uku su fice daga yankinsu ko kuma a yi amfani da karfi a kore su, wannan na zuwa ne sakamkon kisan mutanen al’ummar Nimbo kusan 40 da ake zargin Fulanin sun aikata a Jihar Enugu a kudancin Najeriya.

Fulani sun fara ficewa Enugu kudancin Najeriya
Fulani sun fara ficewa Enugu kudancin Najeriya screammie.com
Talla

Matasan na Ohaneze sun ba Fulanin zuwa ranar Litinin su fice daga yankinsu.

Jaridar Vanguard ta ambato shugabannin kabilar ta Igbo na cewa hare haren Fulani ya tursasawa mata da yara kanana kauracewa gidajensu.

Wannan dalilin ya sa suka dauki matakin bai-daya na ba Fulanin wa’adin su fice daga kasararsu bayan wata ganawa da mambobhin kungiyar suka gudanar na jihohin Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da Delta da Imo da kuma Rivers.

Wannan matakin na matasan kabilar ta Igbo na zuwa ne kafin babbar kungiyar Ohanaeze ta gana kan wannan batu.

Rahotanni dai daga Enugu na cewa Fulani har da Hausawa yanzu haka sun fara ficewa daga yankunan Jihar Enugu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.