An cafke Diezani a London
Rahotanni daga Britaniya sun tabbatar da cewa jami’an tsaro kasar sun cafke tsohuwar ministar albarkatun mai Najeriya Diezani Alison-Madueke a birnin London.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun ofishin jakadancin Birtaniya a kasar Joseph Abuku ya tabbatar da cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a London sun damke Madueke tare da wasu mutane hudu dangane da zargin rashawa a safiyar yau Juma'a a kasar.
Yayin da wasu majiyoyi ke cewa Jami'an Hukumar EFCC na Najeriya sun gudanar da bincike a gidanta dake Abuja a yau.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a jawabinsa na cika kasar shekaru 55 da Yanci kai ya jadada matsayin gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa musamman a bangaren man fetur na kasar.
Buhari wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda zai jagoranci ma'aikatar man Feturi, ya ce gwamnatinsa na samun bayanai akan kudaden da aka sace a ma'aikatar, kuma nan bada dadewa ba za a fara hukunta wadanda ake zargi.
Tun gabanin rantsar da Shugaba Buhari a karagar Mulki, Alison-Madueke ta fice daga kasar zuwa kasashen waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu