Isa ga babban shafi
Najeriya

Ban ga dalilin tsoron gwamnatina ba- Buhari

A jawabin da ya yi wa al’ummar Najeriya a safiyar yau alhamis na cika shekaru 55 da samun 'yancin kai, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya ce babu dalilin da zai sa wani ya ji tsoron gwamanatinsa muddin ba shi da abinda zai boye a kokarin da ya ke yi na dawo da martabar Kasar.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. RFI Hausa
Talla

Shugaba Buhari ya tabo abubuwa da dama, inda ya yi magana game da matakan da ya ke dauka na gyara a kamfanin man fetur na kasar, yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da kungiyar Boko Haram, harma da tallafawa ‘Yan gudun hijira.

Har ilya yau, Buhari ya bayyana dalilin samun jinkiri wajan aika sunayen wadanda ya ke so a matsayin Ministoci ga Majalisar Dattawan Kasar, inda ya dora laifi kan yanayin yadda ya gaji mulki daga tsohuwar gwamanatin da ta shude.

Shugaban ya ce ka da kowa ya ji tsoronsa domin shi bai zo dan ya musgunawa wani ba, sai dai kawai wanda ya san ya aikata laifi ya zargi kansa.

To sai dai a dai-dai lokacin da Najeriya ke murnar cika shekeraru 55 da samun yancin kai, wasu daga cikin 'yan kasar da masana na tafka muhawara kan ci gaban da aka samu a cikin tsawon shekarun da kuma akasin haka.

A hirar sa da sashen hausa na RFI, Farfesa Habu Muhammad na Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya, ya bayyana cewa Najeriya ta samu ci gaba, to sai dai ba yadda ya kamata ba musamman idan aka kwantata da sauran kasashe sa’anninta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.