Isa ga babban shafi
Najeriya

An bankado shirin kai hari a filin tashin jirgin sama a Abuja

Hukumar ‘Yan Sandan farin kaya a Najeriya ta DSS ta gargadi matafiya da suyi taka tsan tsan a filin jirgin saman Abuja bayan ta sanar da bankado wata kungiyar yan ta’adda dake shirya kai hari a birnin.

Filin saukar jirgin Murtala muhammad
Filin saukar jirgin Murtala muhammad naija.com
Talla

Hukumar tace ta kama wani matashi mai shekaru 14 a filin jirgin saman wanda ya amsa laifin cewar an sa shi ne ya sanya ido kan yadda ake hada hada a tashar.

Kakakin hukumar Tony Opuiyo yace suna aiki tare da hukumar tashar jiragen da wasu jami’an tsaro dan dakile duk wani hari da ake shiryawa.

Nijeriya dai na ci gaba da kokarin kawo karshen ayyukan ta’adanci da Kungiyar Boko Haram ke yi acikin kasar abinda ya zama babban barazana ga zaman lafiya a kasar da ma kasashen dake makwabtaka da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.