Isa ga babban shafi
Nigeria

Kotu ta dakatar da sayar da sabbin lambobin mota a Nigeria

A Nigeria, jama’a sun ci gaba da bayyana ra’ayoyin su kan matakin da wata babban kotun kasar ta dauka, na dakatar da hukumar kiyaye haduran kasar, da ta yi kokarin tursasa masu ababen hawa sayen wata sabuwar lamba. Dama hukumar ta yi barazanar cafke duk motar da bata da sabuwar lambarmuhy nan da tsakiyar wannan shekarar.Lokacin da yake yanke hukunci, Alkalin kotun mai shari’ah james tsoho ya ce hukumar kare hadurra ta FRSC bata da da hurumin tilasta wani dreba ya sayi lambar motar.Wani lauya, da ke zaune a birnin Abuja, Barrister Mainasara Faskari, ya ce wannan matakin zai sa Jama’a su amince da ayyukan kotunan kasarComrade Adamu Sulaiman Danzaki, shine jami’in da ke kula da manyan motoci a kungiyar Drebobi ta kasa a Nigeria, ya ce kungiyar tayi shiru ne kan batun sakamakon kai maganar da kotu, da wasu lauyoyi suka yi.Dama a watan Yuni wannan shekarar hukumar ta kiyaye hadurra ta yi barazanar kama duk motar da bata da sabuwar lambar, lamarin da ya sa masu motoci a kasar suka yi ta fadi tashin neman kudin da za su sayi sabuwa lambar. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.