Akalla mutum fiye da 100 ne aka tabbatr sun mutu a hatsarin Mota a yankin kudancin Najeriya
Akalla mutane 100 ne aka tabbatar da mutuwar su a wani mummunan hadarin mota a tarayyar Najeriya, akan hanyar Benin zuwa Lagos.Bayanai sun nuna cewar, hadarin yayi sanadiyar konewar mutane 80 a cikin motoci dabam dabam, 40 da ga cikin su, wadanda suke cikin wata babbar motar safa, da ake kira Luxurious bus.
Wallafawa ranar:
Shaidun gani da Ido sun ce, hadarin ya shafi tankin mai, motar daukar kaya da kuma motocin dake dauke da mutane.
Hadari dai a manyan hanyoyin Nigeria ba wani sabon abu bane, saboda lalacewar hanyoyin, da kuma tukin ganganci.
A wani labarin kuma akalla mutum fiye da Talatin ne aka tabbatar sun mutu, sakamakon hatsarin Motar dakon Man Fetir a wata babbar Hanya a yankin kudancin Najeriya.
Wanan hadarin da yayi sanadin tashin Gobara, ya kuma yi sanadin konewar Gidajen mutane da dama. Akalla mutum 36 ne aka tabbara sun mutu akan hanyar Kauye Ogbogui na jihar Edo, kamar yanda mai Magana da yawun hukumar kiyaye hatsurra ta kasa a tarayyar Najeriya ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP
Sai dai akwai bayannan dake nuna cewar akwai wasu kalilan da aka ceto da Ransu a cikin wannan hatsari
Hatsarin dai ya auku ne akan babbar Hanyar data hada yankin kudu maso Gabashin kasar da kuma birnin Lagas dake a yankin kudu maso Yammacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu