Isa ga babban shafi

Yaki da Covid-19 ya hana bai wa yara miliyan 67 rigakafin cutuka- UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya koka yadda kananan yara akalla miliyan 67 suka gaza samun cikakken rigakafi tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021 saboda yadda bangarorin lafiya suka mayar da hankali wajen yaki da annobar cutar Covid-19.

UNICEF ta ce abin takaici ne yadda annobar ta Covid-19 ta mayar da kokarin da ake na kare yara daga kamuwa da cutuka masu hadari baya.
UNICEF ta ce abin takaici ne yadda annobar ta Covid-19 ta mayar da kokarin da ake na kare yara daga kamuwa da cutuka masu hadari baya. © UNICEF
Talla

Cikin rahoton shekara shekara da UNICEF kan fitar game da halin lafiyar kananan yara wanda na bana ta yi masa lakabi da makomar lafiyar kananan yara a 2023, ta ce an samu mummunan koma baya a bangaren kula da lafiyar yara.

A cewar UNICEF abin takaici ne yadda hankula suka karkata kan yaki da cutar ta Covid-19 amma aka manta da yakar cutuka mafiya hadari ga kananan yaran da kan haddasa asarar dimbin rayuka.

Asusun ya bayyana cewa Covid-19 babbar annoba ce da ta hautsina tsarin rigakafin kananan yara wanda ya sa ta mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na ganin kowanne yaro ya samu cikakken rigakafi.

Alkaluman da UNICEF ta fitar sun nuna cewa annobar ta Covid-19 ta mayar da matsayar rigakafin kananan yara a Duniya zuwa halin da ake ciki a shekarar 2008 wanda ke nuna samun mummunan koma baya.

Rahoton ya bayyana cewa tsakanin 2019 zuwa 2021 adadin kananan yaran da ba a yiwa rigakafi bay a tashi daga miliyan 13 zuwa miliyan 18 wanda ke nuna karuwar fiye da kashi bisa uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.