Isa ga babban shafi

Kwararru sun bukaci kiyaye tsaftar abinci don dakile yaduwar cututtuka

Wani rahoton hadin gwiwa tsakanin cibiyar binciken bunkasa kiwon dabbobi ta duniya ILRI, da kuma shirin Lafiya na kasa da kasa kan tabbatar da tsaftar abinci da ruwan sha, ya ce akwai bukatar tsara sabbin dabarun dakile yaduwar cutuka saboda rashin tsaftar abinci da sauran kayan masarufi a kasashe masu tasowa. 

Masana na gargadin cewa akwai bukatar a bullo da sabbin matakan tunkarar kalubalen da ke tafe.
Masana na gargadin cewa akwai bukatar a bullo da sabbin matakan tunkarar kalubalen da ke tafe. AFP
Talla

Muhimmin abinda rahoton ya kunsa shi ne bayanan yadda kananan ‘yan kasuwa da suka hada da masu sarrafa  abinci, da kayan gwari, da masu tallata su a kasuwannin kasashe marasa karfi fiye da 20, ke da tasiri wajen kiyaye tsaftar abinci da kuma dakile yaduwar cutuka daga nau’ikan cimakar, yayin aiwatar da ayyukansu na yau da kullum.  

Wasu daga cikin muhimman nau’ikan abincin da lamarin ya shafa dai sun hada da nama, da kifi, da kayan marmari da kuma ganyayyaki. 

Rahoton ya bayyana rashin tsafta, rashin ingantattun hanyoyin adana abinci da hanyoyin shirya shi, da kuma karancin kayayyakin more rayuwa da yanayin muhalli, a matsayin abubuwan da ke haifar da matsalar yaduwar cutuka a dalilin abinci maras inganci. 

Sai dai a cewar masu binciken, wani abin takaici shi ne, yadda kasashe kadan ne ke da dabarun zamani na dakile hatsarin na barkewar cutuka saboda gurbacewar nau’ikan abinci. 

Domin shawo kan matsalar, rahoton ya bukaci hukumomi da su fara wayar da kan al’ummominsu kan hanyoyin sarrafa nau’ikkan abinci cikin tsafta, tun daga matakin unguwanni. Sai kuma inganta yanayin muhalli da tsaftarsa, da kuma samar da ruwan sha mai tsafta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.