Isa ga babban shafi

Ghana ta sanya dokar hana zirga-zirgar dabbobi saboda bullar wata cuta

Gwamnatin kasar Ghana ta sanya dokar hana zirga-zirgar kananan dabbobi da kuma shanu na tsawon wata guda a gabashin kasar, sakamakon rahoton barkewar cutar sankarau ta dabbobi da ake kira anthrax da aka samu a sassan yankin.

Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna.
Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna. AFP/Getty Images - Stefan Heunis
Talla

Wasu daga cikin wuraren da dokar ta shafa sun hada da karamar hukumar Bawku, da Bawku West, da Pusiga, da Garu, da Tempane, da kuma Gundumar Binduri.

A makon da ya wuce, an samu rahoton mutuwar shanu bakwai, da awakai 23 a gundumomin Bansi da Sapeliga.

Haka zalika, hukumomin lafiya, sun tabbatar da cewa akwai mutum 13 da suka harbu da wannan cuta, har ma ta yi ajalin mutum guda a gundumar Bansi.

Yanzu haka an dauki samfurin mutum 11 zuwa dakin gwaji na Pong-Tamale.

Tuni hukumomi suka bayar da umarnin yi wa dabbobi rigakafin cuta ga dukkanin dabbobin da ke yankin gundumar Bansi da Sapeliga.

Babban daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasar, Alhaji Abubakari Inusah, y ace tuni aka dauki matakan gaggawar tunkarar wannan annoba, bayan taron gaggawa da suka gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.