Najeriya ta amince da rigakafin zazzabin cizon sauro
Yayin da ayau ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na duniya, Nigeria ta zamo kasa ta biyu a yankin Afrika bayan Kasar Ghana da data amince da ta yi amfani da sabuwar Allurar yaki da cutar wanda aka yi wa lakabi da R-21.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:01
Wannan ya biyo bayan gwaje-gwajen da ta ce ta yi ne, domin tabbatar da sahihancin allurar.
A shekarar 2021 cutar malaria ta kashe mutane 619,000, wanda kusan kashi 96% na zaune a Afirka.
Sama da mutane biliyan 1.6 ne suka kamu da zazzabin cizon sauro da kuma mutuwar mutane miliyan 11 a yankin Afirka daga 2000-2021 in ji WHO.
Shiga alamar sauti domin sauraron rahoton Muhammad Kabiru Yusuf.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu