Isa ga babban shafi

WHO da AU sun bukaci daukar matakan gaggawa don kawar da tarin fuka a Afrika

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da kungiyar kasashen Afirka ta AU sun bukaci daukar matakan gaggawa domin kawo karshen yadda yara kanana ke kamuwa da cutar tarin fuka ko ‘tuberculosis’. Wadannan hukumomi biyu sun gabatar da sanarwar hadin gwuiwa ne tare da Cibiyar Elizabeth Glaser Pediatric da kuma kungiyar ‘Stop TB Partnership’ wajen taron ministocin lafiyar kasashen Afirka da ke gudana a Lome.

Cutar ta tarin fuka na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a nahiyar Afrika.
Cutar ta tarin fuka na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a nahiyar Afrika. REUTERS - Luke MacGregor
Talla

Alkaluma sun nuna cewar nahiyar Afirka na dauke da kasashe 17 daga cikin kasashen duniya 30 da ke dauke da adadin masu fama da cutar tarin fuka mafi yawa a duniya, wanda daga cikin su ake da yara dubu 322 da ke tsakanin shekara guda zuwa 15 da ke dauke da ita, adadin da shi ne kashi guda bisa 3 a duniya baki daya.

Hukumomin sun ce abin takaici shi ne kashi biyu bisa 3 na yaran da ke dauke da wannan cuta, ba a musu gwaji domin gano suna da ita, har zuwa lokacin da za ta musu illa.

Kwamishiniyar lafiya da jin dadin jama’a ta kungiyar kasashen Afirka ta AU, Minata Samate Cessouma, An bayyana cewar kashi 19 na na masu fama da cutar a duniya, na da alaka da rashin abinci mai gina jiki, abinda ke zafafa cutar.

Daraktar Hukumar Lafiya ta Duniya mai kula da shiyar Afirka, Dr Matshidiso Moeti ta ce an dade ana kauda ido akan yaran Afirka da ke kamuwa da cutar, inda ta bayyana fatar wannan kira zai zaburar da nahiyar daukar matakin ganin cewar babu wani yaro a Afirka da ya mutu sakamakon cutar da aka kawar da ita a wasu kasashen duniya.

Jami’ar ta ce za a samu wannan nasara ce kawai ta hanyar samun goyan bayan shugabannin siyasa da kuma taimakon kasashen duniya wajen samar da kayayyakin gwaji da kuma magungunan yaki da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.