Isa ga babban shafi
Lafiya

Ana bukatar biliyoyin Dala don yaki da cutar HIV

Asusun kula da lafiya na duniya, ya ce akalla dala biliyan 18 ne ake bukata don dawo da yaki da cutar zazzabin cizon sauro, tarin fuka da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, bayan da annobar coronavirus ta haifar da koma baya ga shirin kawo karshen wadannan cutuka.

An samu koma-baya wajen yaki da cutar HIV saboda bullar cutar Korona
An samu koma-baya wajen yaki da cutar HIV saboda bullar cutar Korona GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP/File
Talla

Sanarwar da Asusun ya fitar ta ce daga 2024 zuwa 2026 ana bukatar akalla sama da dala biliyan hudu, fiye da abin da aka tarawa asusun yaki da cutar sida ko kuma HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro a shekarar 2019.

Daraktan asusun Peter Sands, ya ce nufin samar da dala biliyan sha takwas shine kara damarar yakar cutukan ta hanyar gwaji da rigakafi da kuma ita kanta annobar.

A watan Satumban 2020, rahoton ya nuna cewa adadin mutanen da ke fama da cutar tarin fuka a cikin kasashen da ake aikin agaji ya ragu da kashi goma sha tara kuma shirye-shiryen rigakafin cutar HIV ya ragu da kashi goma sha daya.

Cutar tarin fuka ta yi sanadiyar mutuwar mutane miliyan daya da dubu dari biyar a 2020 kadai a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, mafi girma da ke salwanta rayuka a kowace shekara kafin barkewar cutar Covid19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.