Isa ga babban shafi
Lafiya-Mata

Tada komadar nono: TUV ta Jamus za ta biya dubban Mata diyyar yi musu illa

Wata Kotu a Faransa ta samu hukumar kula da ingancin kayayyakin da ake sarrafawa ta kasar Jamus da ake kira TUV Rheinland da laifin amincewa da wani sinadari da ake amfani da shi wajen tada komadar nonon mata wanda daga bisani ya yiwa dubban matan illa.

Nau'in sinadarin da ake amfani da shi wajen tayar da komadar nono.
Nau'in sinadarin da ake amfani da shi wajen tayar da komadar nono. REUTERS - Eric Gaillard
Talla

Kotun ta yanke hukuncin cewar ya zama wajibi wannan Hukuma ta TUV Rheinland da ke Jamus ta biya diyya ga dubban matan da suka gamu da illa bayan an musu aikin tayar da komadar nonon wajen sanya musu sinadarin wanda hukumar ta sahale amfani da shi.

Wannan hukunci da ke zuwa bayan kwashe sama da shekaru 10 ana tafka shari’a zai bude kofa ga dubban matan da suka samu illa wajen aikin sanya musu sinadarin karbar diyya daga hukumar saboda amfani da sinadarin da kamfanin Faransa na ‘Poly Inplant Prothese’ ke samarwa.

Rahotanni sun ce akalla mata sama da dubu 400 suka yi amfani da sinadarin a kasashen duniya, kuma akasarin su sun fito ne daga kasashen da ke yankin kudancin Amurka.

Bayanai sun ce wannan sinadari kan fashe a jikin matan da kuma sanya nonon ya kumbura har zuwa lokacin da za a cire shi.

Kotun ta ce Hukumar TUV ta yi sakaci saboda haka ya zama dole a ladabtar da ita.

Akalla mata sama da dubu 20 suka shigar da karar kamfanin samar da sinadarin abinda ya sa gwamnatin Faransa ta haramta amfani da shi a shekarar 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.