Isa ga babban shafi
WHO-China

WHO ta amince da sahihancin rigakafin Sinopharm samfurin China

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta amince da sahihancin allurar rigakafin Covid-19 samfurin Sinopharm wanda kasar China ta sarrafa, tare da bai wa kasashe damar yin amfani da shi a kan al’ummominsu.

Rigakafin Covid-19 na China Sinopharm.
Rigakafin Covid-19 na China Sinopharm. REUTERS - THOMAS PETER
Talla

Kafin amincewa da wannan magani da kasar China ke sarrafawa, tuni hukumar ta lafiya ta amince da wasu magungunan da ake amfani da su domin kariya daga cutar, da suka hada da BioNtech, Moderna, Johnson and Johnson da kuma AstraZeneca.

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce za a yi amfani da maganin na Sinapharm ne a matsayin wucin gadi lura da halin da duniya ke ciki saboda tsanantar annobar ta korona.

A taron manema labaran da ya gudanar a wannan juma’a, Gebreyesus ya ce Kwamitin Kwarurru kan ingancin allurar rigakafi da ke karkashin hukumar ta lafiya, ya ce ana iya amfani da wadannan magunguna a kan kowane rukuni na jama’a matukar dai sun kai shekaru 18 a duniya ko fiye da haka.

Kafin amincewar hukumar ta lafiya, tuni aka fara amfani da allurar da China ke sarrafawa a cikin kasashen duniya 42, sai AstraZeneca a kasashe 166, Pfizer-Biontech kasashe 94, sai kuma Moderna a kasashe 46.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.