Lafiya-MDD
Kashi 90 na Al'ummar duniya na shakar gurbatacciyar iska
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin ko wadanne mutane 10 da ake da su a duniya, 9 na shakar gurbatacciyar iska abinda ke kai ga mutuwar mutane sama da miliyan 6 kowacce shekara.
Wallafawa ranar:
Talla
Maria Neira, shugabar sashen kula da muhalli da kuma lafiyar jama’a ta ce wadanan bayanai sun isa su ta da hankalin al’umma.
Jami’ar ta ce an fi samu gurbacewar iskar a kasashe matalauta, amma matsalar gurbacewar muhalli ta shafi kowacce kasa.
An dai gudanar da binciken ne a garuruwa 3,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu