Isa ga babban shafi
Zika

Zika na lalata kwakwalwar jarirai da manya

Wani binciken kwararru masana na kasar Faransa ya nuna cewa cutar Zika wadda a ke kamuwa da ita sakamakon cizon sauro na kai ga lalata kwakwalwar jarirai har da manya.

Masu bincike kan cutar Zika sun ce, cutar na shafar kwakwalwar manya mutane
Masu bincike kan cutar Zika sun ce, cutar na shafar kwakwalwar manya mutane REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

Masanan sun gano wani dattijo mai kimanin shekaru 81 da ya kamu da cutar bayan ya dawo daga wani dogon yawon bude ido yayin da a yanzu ya ke samun kulawa a wani asibiti da ke kusa da birnin Paris na Faransa.

Cutar dai ta kai ga shafar kwakwalwar dattijon kamar yadda masu binciken suka wallafa a mujallar New England wadda ke rawaito labaran da suka shafi kiwon lafiya.

Wannan ne karo na farko da aka samu rahoton da ke cewa cutar ta Zika ta shafi kwakwalwar wani babban mutum kamar yadda Guillaume Carteaux  daya daga cikin mawallafan kuma jami'in kiwon lafiya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.