Isa ga babban shafi

Kasashen Kudancin Amurka na taron samar da kariya ga gandun dajin Amazon

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da takwarorinsa na kudancin Amurka sun bude wani taro na kwanaki biyu a ranar Talata, kan yadda za a shawo karshen matsalolin da ake addabar gandun dajin nan mafi girma a duniya wato Amazon, yayin da masana muhalli ke gargadin irin kalubalen da ke tunkarar yankin.

Tawagar wakilan kasashen kudancin Amurka, yayin taron koli kan yadda za a kawo karshen sare dazuka da ke haifar da koma baya ga shirin kare muhalli a duniya.
Tawagar wakilan kasashen kudancin Amurka, yayin taron koli kan yadda za a kawo karshen sare dazuka da ke haifar da koma baya ga shirin kare muhalli a duniya. AP - Eraldo Peres
Talla

Hukumomi a Brazil sun sha alwashin nemo wata dabara mai cike da kishin kasa don dakatar da sare itatuwa a wannan taro na kwanaki biyu da kungiyar kasashen Amazonia suka shirya a Belem.

Wannan dai shi ne taron koli na farko cikin shekaru 14 na kungiyar kasashe takwas da aka kafa a shekarar 1995 wadanda suka kunshi kasashen kudancin Amurka da ke kusa da yankin Amazon da suka hada da Bolivia da Brazil da Colombia da Ecuador da Guyana da Peru da Suriname da kuma Venezuela.

Yankin da aka kiyasta na dauke da kashi 10 cikin 100 na halittun duniya, da suka hada da mutane miliyan 50 da kuma biliyoyin itatuwa, ya kasance muhimmin wuri da ke bayar da gudun mowa wajen rage dumamar yanayi.

Abin da ya sanya masana kimiyya yin gargadin cewa sare bishiyoyi na kara jefa gandun dajin cikin hatsari, wanda hakan mummunar illa zai haifar ga Shirin yaki da dumamar yanayi.

Kasashen yankin sun kuduri aniyar ba za su bar Amazon ya kai ga gaza magance matsalar dumamar yanayin ba, in ji ministar muhalli ta Brazil Marina Silva a wani taron ministoci gabanin taron.

Ministan harkokin wajen Brazil Mauro Vieira ya ce taron zai fitar da sanarwar hadin gwiwa da ke kunshe da umarni ga kasashen 8 da su aiwatar da sabbin tsare-tsare da sabbin ayyuka na kare dazuzzukan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.