Isa ga babban shafi
Brazil

Yawan wadanda suka mutu a ambaliyar ruwan Brazil ya haura 116

Masu aikin ceto a Brazil na cigaba da neman masu sauran rai cikin laka da baraguzan gine-gine, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa, da zabtarewar kasa a birnin Petropolis, a daidai lokacin da kawo yanzu adadin wadanda suka mutu a iftila’in ya karu zuwa mutane 117

Yankin da lamarin ya auku a Brazil
Yankin da lamarin ya auku a Brazil Florian PLAUCHEUR AFP
Talla

Har yanzu dai jami’an ceto na lalauben gwamman mutanen da suka bace, yayin da kuma ake fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu.

Guguwar dai ita ce ta baya bayan nan da ta afkawa Brazil cikin watanni ukun da suka gabata, masifun da masana suka ce sauyin yanayi ne ke kara ta'azzara su.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta Petropolis ta ce an ceto akalla mutane 24 da ransu.

Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Taklatar nan.

Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.