Isa ga babban shafi

Kotu ta haramtawa tsohon shugaban Brazil shiga harkokin siyasa na shekaru 8

Alkalan babbar kotun sauraron kararrakin zabe ta Brazil, sun kada kuri’ar haramta wa tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro mai ra'ayin rikau, shiga harkokin siyasa na tsawon shekaru takwas, biyo bayan sukar tsari da kuma sahihancin zaben kasar ta Brazil da tsohon shugaban ya rika yi. 

Tsohon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro.
Tsohon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro. REUTERS - ADRIANO MACHADO
Talla

Hudu daga cikin alkalai bakwai na babbar kotun zaben ne suka kada kuri'ar kakaba wa Bolsonaro takunkumi hana shi siyasar, yayin da Alkali daya ya goya masa baya, ragowar masu shari’a biyu kuma basu bayyana matsayinsu ba. 

Bolsonaro bai halarci zaman kotun ba, inda ya tafi Belo Horizonte da ke kudu maso gabashin kasar, don gudanar da liyafar cin abincin rana tare da mambobin jam'iyyarsa ta Liberal.

Kotun dai ta yi shari’ar Bolsonaro mai shekaru 68 a duniya, kan wani taron da ya yi ta kafar talabijin da jami’an diflomasiyyar kasashen waje a watan Yulin 2022, watanni uku kafin ya sha kaye a zaben kasar.

Da wannan hukuncin kotu, Bolsonaro ba zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasar na shekara ta 2026 ba, wanda zai baiwa wasu sababbin fuskoki damar takarar shugabancin kasar ta Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.