Isa ga babban shafi

Alberto Fernandez ya cire kansa daga cikin 'yan takara a zaben kasar

Shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez ya sanar cewa ba za ya sake shigar da takarar sa a  zabe na watan Oktoba mai zuwa ba,don haka ya hakura da kare tarihinsa a rumfunan zabe a kan koma baya ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki da karuwar talauci, duk da ci gaban shekaru biyu.

Shugaban kasar Argentina  Alberto Fernández.
Shugaban kasar Argentina Alberto Fernández. REUTERS - DANIEL BECERRIL
Talla

A wani bidiyo a shafin Twitter,Shugaban kasar Alberto Fernandez ya ba da sanarwar cewa ba zai  tsayawa takarar shugabancin kasa karo na biyu a watan Oktoban wannan shekara.

Shugaban mai ci yak arasa da cewa ‘ ranar 10 ga Disamba 2023 , zan mika wa duk wanda aka zaba bisa gaskiya mulki.

 Zan yi aiki tukuru domin ya zama abokin aiki a fagen siyasarmu”.

Mataimaikiyar Shugaban kasar Argentina Cristina Kirchner
Mataimaikiyar Shugaban kasar Argentina Cristina Kirchner REUTERS - AGUSTIN MARCARIAN

Al’amarin da ya jibanci hauhawar farashin kayakin masaruhi wanda ya zarce kashi 100% ya janyo masa fushin jama’a.

A wani lokaci reshen hagu na haɗin gwiwar Frente de Todos Peronist, a kai a kai suna sukar sa, sun shafe makonni da yawa suna matsawa Shugaban kasar Alberto Fernandez na ya kaucewa tsayawa takara.

Shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez
Shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez AP - Markus Schreiber

 Eduardo de Pedro, ministan cikin gida na kusa da mataimakiyar shugaban kasa Cristina Kirchner, ya yi marhaba da matakin Shugaban kasar Alberto Fernandez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.