Isa ga babban shafi
Thailand

Dakarun gwamnati na ci gaba da sasakar masu zanga zanga

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dakarun gwamnatin kasar Thailand da masu zanga zanga a Bangkok babban birnin kasar, inda aka diba wa masu zanga zangar wa’adin ficewa daga sansani da suke ciki.Tun barkewar rikici bayan tura dakaru ranar Alhamis data gabata kimanin mutane 37 suka hallaka yayin da wasu kimanin 250 da suka samu raunika. Daya daga cikin manyan habsoshin sojan kasar Janar Khattiya Sawasdipol, wanda ya bijire ya koma bangaren masu zanga zanga, ya rasa ransa yau Litinin sakamakon harbin sad a aka yi cikin kwanaki da suka gabata.Gwamnatin kasar ta Thailand ta ce zata gudanar da tattaunawa da masu zanga zangar sanye da jajaye kaya, muddun suka amince da ficewa daga cikin sansanin da suke ciki. Amma anasu bangaren shugabannin masu zanga zangar sun nemi samun saka idon Majalisar Dinkin Duniya yayin tattaunawar tare da janye dakarun sojan da suke kokarin murkushe zanga zangar.Babban burin masu zanga zangar shine Prime Minista Abhisit Vajjajiva ya yi murabus tare rusa majalisar dokokin kasar, sannan ya kira zabe cikin gagggawa.Gwamnatin kasar ta Thailand ta aiyana dokar ta baci cikin yankunan kasar 22, domin tabbatar da cewa rindinar soja ta shawo kan matsalar, tare da dakatar da masu neman zuwa Bangkok babban birnin kasar da nufin kara karfin masu zanga zangar. Ana tsautta zaton cewa akwai kimanin masu zanga zangar 5,000 da gwamnati ke neman ganin sun kama gabansu kafin cikar wa’adin da aka diba musu.

Reuters / Cyrille Andres
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.