Isa ga babban shafi
Thailand

Rikici ya kara kamari tsakanin masu zanga zanga da jami’an tsaro

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin masu zanga zangar kasar Thailand da jami’an tsaron dake yunkurin killace su a Bongkok babbab birnin kasar. An kulle ofisoshin jakadancin kasashe, yayin da masu zanga zangar suka kara da jami’an tsaro abunda ya yi sanadiyar mutuwar mutun daya cikin artabun tsakiyar dare.Masu zanga zangar suna bukatar Prime Ministan kasar ta Thailand Abhisit Vejjajiva ya yi murabus, rusa majalisar dokoki tare da kirar zabe cikin gaggawa.Akasarin masu zanga zanagr sanye da jajayen kaya magoya bayan hambararren Prime Minista Thaksin Shinawatra ne, da aka kifar da wamnatinsa cikin shekara ta 2006.A yau Jumma’a Thaksin ya yi kira ga gwamnatin kasar ta janye dakarun da zuba, domin shawo kan zanga zangar. Ya nemi Prime Minista Vejjajiva ya janye janye dakarun tare dage dokar ta bacin da aka saka, sannan ya nemi samun gudanar da sasantawa ta kasa baki daya.

Masu zanga zanga sanye da jajayen kaya dake Bangkok babban birnin kasar Thailand
Masu zanga zanga sanye da jajayen kaya dake Bangkok babban birnin kasar Thailand REUTERS/Jerry Lampen
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.