Isa ga babban shafi
Thailand

An Harbi Wani Habsan Soja

An harbi habsan sojan dake baiwa masu zanga zangar kasar Thailand shawara, yayin da aka ji aman harsasai masu sarrafa kansu a cibiyar kasuwanci Bangkok babban birnin kasar.Khattiya Sawasdipol wanda rindinar sojan kasarta dakatar, masanin harkokin tsaro an garzaya da shi zuwa abisiti bangare masu jin jiki sosai.An shawarci mutane su watse daga yankin kafin wa’adin da aka diba ya cika tun da fari.Rindinar sojan kasar ta Thailand ta ce zata tura karin dakaru da tankokin yaki, domin kewaye masu zanga zangar dake ci gaba da nuna turjiya.Kakakin rindinar sojan kasar Sansern Kaewkamnerd ya ce jami’an dake da alhakin warware rikicin zasu majalisar zartaswa ta saka dokar ta baci cikin yankuna 15 da masu zanga zangar ke da karfi.

Masu zanga zangar kasar Thailand yayin artabu da jami'an Soja
Masu zanga zangar kasar Thailand yayin artabu da jami'an Soja REUTERS/Steve Pace
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.