Isa ga babban shafi
Kyrgyzstan

Gwamnatin Rikon Kwarya ta fara neman Hambararren Shugaba

Gwamnatin rikon gwaryar kasar Kyrgyzstan ta yi alkawarin bada kudade ga bayyana da za su taimaka ta cafko hambarren shugaban kasar Kurmanbek Bakiyev da jiga jigan gwamnatinsa. Bakiyev tare da iyalensa sun tsere zuwa kasar Belarues bayan kifar da gwamnati yayin boren yan adawa ranar bakwai ga watan Afrilu, kuma yanzu gwamnatin rikon kasar karkashin jagorancin Roza Otunbayeva ta na tuhumar tsohuwar gwamnatin da mutuwan mutane 85 masu zanga zanga.A cikin bayan gwamnatin rikon kasar ta Kyrgyzstan, ta bayyana mutanen da ake nema da su ka hada da dan tsohon shugaban, da yan uwansa uku tare da Prime ministansa Daniyar Usenov, kma akwai kimanin kudade dala dubu 100, ga bayanan da za su taimaka wajen kamo mutanen.

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.