Isa ga babban shafi
Argentina

Argentina-An daure tsohon shugaban kasar a gidan yari

Kotun kasar Argentina ta daure tsohon shugaban kasar, Reynaldo Bignone Dan shekaru 82, na tsawon shekaru 25 a gidan fursuna. Kotun dake Boenos Aires babban birnin kasar ta samun tsohon shugaban, wanda ya yi mulkin kama karya da laifin bada umurni cin zarafin mutane da tsarewar da ta saba ka’ida.Akwai wasu tsaffin jami’an wannan gwamnati shida da aka yanke musu zaman gidan wakafin na lokuta daban daban.Bignone ya karbi ragamar tafiyar da kasar cikin shekarar 1982, bayan kasar ta Argentina ta gwabza yaki da kasar Biriotaniya akan Tsibirin Falkland. Yan ada sun ce akwai mutane dubu 40 da suka bace lokacin mulkinsa, cikin yanayin mai tararrabi. Mulkin Reynaldo Bignone ya kawo karshe a shekarar 1983.

Reynaldo Bignone,
Reynaldo Bignone, Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.