Isa ga babban shafi

Isra'ila ta fara aikin gina yankin tsaro a iyakarta da Gaza

Rundunar sojin Israila ta fara aikin gina  yankin tsaro na tsawon sama da rabin mil a ilahirin kewayen kan iyakarta da Gaza mai kimanin mil 37, kuma wannan yanki zai kasance ne a bangaren Gaza, wanda dakarun Isra’ila ne kawai za a bai wa damar shiga ciki.

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. via REUTERS - POOL
Talla

A farkon watan Disamban shekarar da ta gabata ne Isra’ila ta shaida kasashen Larabawa a yankin Gabas ta Tsakiya aniyarta ta gina wannan yankin tsaro a tsakanin Gaza da Isra’ila daga arewa da kudu don kare kanta daga hare-haren Hamas ko ma wata kungiyar ‘yan ta’adda da za su iya far musu.

 

Zalika, a watan Nuwamba ma sai da fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da sakataren tsaron Amurka  Antony Blinken Amurka a kan wannan batu, wanda  ya ce zai yi matukar amfanni a wajen inganta tsaron kasar ta Yahudu bayan wannan yaki da ke gudana.

 

Sai dai kakakin majalisar Tsaron Amurka John Kirby, ya fito a ranar 1 ga watan Disamba yana cewa Amurka ba ta marhabun da duk wani mataki da zai rage girman kasa na Gaza, yana mai cewa dole Zirin ya ci gaba da kasancewa yanki Falasdinu.

 

Mai ba da shawara ga Netanyahu a fannin tsaro, Ophir Falk, ya ce matakin da Isra’ila ke dauka yana cikin wani shiri ne mai sala uku, wanda ya kunshi kawar da kungiyar Hamas, kawar da masu dauke da makamai a Gaza tare da sauya tunanin al’ummmarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.