Isa ga babban shafi

Ba za a amince da tauye damar Falasdinawa ta samun kasarsu ba - MDD

Magatakardan Mjalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce dole ne a yi la’akari da damar Falasdinawa ta kafa kasarsu mai yanci, yana mai cewa hana su kafa kasarsu abu ne da ba za a amince da shi ba.

Antonio Guterres, Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya. AP - Gian Ehrenzeller
Talla

Ya bayyana haka ne a yayin jawabin da ya  gabatar abtaron kungiyar kasashe ‘yan ba -ruwanmu da aka yi a Uganda a jiya Asabar.

 

Ya ce dakile wa Falasdinawa damar samun kasarsu zai tsawaita rikici, wanda zai zame wa ilahirin duniya barazana, ta wajen kawo rarrabuwar kawuna.

 

A ranar Juma’a fadar gwamnatin Amurka ta White House ta sanar da cewa shugaba Joe Biden ya jaddada goyon bayan samar da kasar Falasdinu mai ‘yanci a yayin wata ganawa tsakanin sa da Fira minista Benjamin Netanyahu.

 

Bayan haka ne Netyanyahu din ya fito fili ya yi watsi da matsayin Joe Biden a game da samar da kasar Falasdinu mai ‘yanci.

 

A ranar 7 ga watan Oktoba ne fada ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas, bayan harin da mayakan Hamas din suka kai cikin kasar Yahudu, lamarin da ya  yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu daya.

 

Tun daga wannan lokaci ne Isra’ila ta yi ta luguden wuta a kan Zirin Gaza, a kokarin da ta ce tana yi na kakkabe mayakan Hamas, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane kusan dubu 25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.