Isa ga babban shafi

Shugaban Amurka ya jaddada goyon baya ga batun samar da kasar Falasdinawa

Shugaban Amurka, Joe Biden ya shaida wa Fira ministan Isra’ila cewa har yanzu yana goyon bayan samar da kasar Falasdinu mai yanci a nan gaba, kamar yadda wata sanarwa daga mfadar White House ta bayyana, biyo bayan ganawar shugabannin biyu a jiya Juma’a. 

TECH-EU/USA
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - LEAH MILLIS
Talla

Kakakin majalisar tsaron Amurka John Kirby ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu shugaba Biden ya yi amannar za a samar da kasar Falasdinu, sai dai ya  ce hakan na bukatar aiki tukuru. 

Kirby ya ce Biden ya kuma yi na’am da shawarar Isra’ila ta barin a shigar da hatsi Zirin Gaza, duk ad rikicin da ke gudana tsakaninta da mayakan Hamas.

Wannan na zuwa ne biyo bayan tankiya da ke ci gaba da ta’azzara tsakanin kasashen biyu a kan yakin da Isra’ila ke ci gaba da gwabzawa da Hamas a yankin zirin Gaza. 

Tun da farko a wanan Juma’a, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kudirin da ke neman bai wa yankin Falasdinu damar zama kasa mai cin gashin kanta, wanda kasashe ke kallo a matsayin hanya daya tilo da za ta kawo karshen rikicin tsawon shekaru da bangarorin biyu suka shafe suna yi.

 

Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da tsananta farmaki a yankin Gaza don kamala ceto ilahirin fursunonin Isra’ilan da Hamas ta kame tun ranar 7 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.