Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kashe yan jarida 79 a Gaza, ciki har da wakilin AFP

Isra’ila ta sake hallaka karin jami’an yada labarai biyu a wani hari da ta kai tsakiyar Gaza ciki kuwa har da wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Wasu daga cikin iyalan 'yan jaridar da aka kashe
Wasu daga cikin iyalan 'yan jaridar da aka kashe REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Rahotanni sun ce makami mai linzami ne ya dira kan motar da suke ciki tare da abokin aikin sa Hamza Wael Al- Dahdouh, wakilin gidan talabijin na Al-Jazeera.

Hamza shine da daya tilo da ya rage cikin iyalan gidan mahaifin sa Wael wanda shine shugaban ofishin gidan talabijin na Al-Jazeera da ke Gaza.

Wata guda da suka wuce ne harin Bam na Isra’ila ya kashe kafatanin iyalan Wael sai dansa Hamza ne kadai ya tsira kuma shima a wannan rana Isra’ilan ta yi ajalin sa.

Bayanai na cewa kawo yanzu hare-haren Isra’ila sun yi ajalin ‘yan jarida 79 tun bayan fara yakin a watan Octoban da ya gabata.

 

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da dakarun Isra’ila ke kara matsa hare-hare a yamma da kogin Jordan, yayin da take ikirarin kakkabe mayakan Hamas.

Wannan shine kutse mafi muni da Falasdinwan yamma da kogin Jordan suka taba gani sama da shekaru 30 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.