Isa ga babban shafi

Karin kamfanonin jiragen ruwa sun dakatar da balaguro ta tekun Red Sea

Karin wasu kamfanonin sufurin jiragen ruwa biyu sun sanar da dakatar da zirga – zirga ta tekun Red Sea, wanda ke da matukar mahimmanci ga kasuwancin kasa-da-kasa, biyo bayan hare haren ‘yan tawayen Houthi na Yemen a yankin.

Jirgin ruwan dakon sandukai a kamfanin CMA CGM.
Jirgin ruwan dakon sandukai a kamfanin CMA CGM. AFP - SAMEER AL-DOUMY
Talla

Sanarwa da kamfanin sufurin ruwa na kasar Italiya da Switszerland, MSC da na Faransa CMA  CGM suka bayar  ta biyo bayan irin ta da kamfanonin Maersk da Hapag-Lloyd suka bayar ne a ranar Juma’a.

Wannan na zuwa ne biyo bayan gargadin da ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, wadanda ke iko da akasarin kasar Yemen suka bayar.

Kungiyar ‘yan tawayen Houthi ta ce tana kai wa jiragen ruwa hare-hare a kusa da mashigin Bab al-Mandeb ne don ta  matsa wa Isra’ila lamba a kan yakin da take da Hamas a  Gaza.

Dubban jiragen ruwa ne ke bi ta wannan masigi a duk shekara.

Wannan lamari ya  ta’azzara fargabar cewa wannan rikici na Gaza na iya  bazuwa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.