Isa ga babban shafi

Akalla mutane dubu 8 ne suka bace a cikin baraguzan gine-gine a Gaza

Sama da mutane dubu 8 ne suka bace a cikin baraguzai sakamkon haren-haren da Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza ba kakkautawa, kuma kashi 70 daga cikinsu mata da yara kanana ne, kamar yadda Hamas ta bayyana.

Baraguzan gine-ginen da hare-haren Isra'ila suka ruguje a  yankin Rafah na Gaza.
Baraguzan gine-ginen da hare-haren Isra'ila suka ruguje a yankin Rafah na Gaza. AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Mahukuntan yankin Gaza sun ce, yayin da wannan yaki ya shiga kwana na 70, adadin wadanda suka samu rauni ya kai dubu 51.

Adadin Falasdnawa da suka mutu a sakamakon wadannnan hare-hare da Isra’ila ta fara kai wa a matsayin martini ga harin da Hamas ta kai mata ya zuwa yanzu ya  kai dubu 18 da dari  8.

 A wayewar garin Lahadin nan Isra’ila ta ci  gaba da luguden wuta  a kan Gaza, a yayin da mahukuntanta ke shan matsin lamba daga ‘yan uwan wadanda Hamas take garkuwa da su yau sama da watanni biyu kenan.

Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da yakkin da ta ce tana yi da Hamas, yakin da ta  bayyana a matsayin kokarin tabbatar da wanzuwarta a matsayin al’umma, tana mai cewa sai ta gai  ga nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.