Isa ga babban shafi

Isra'ila na shan matsin lamba kan ceto wadanda Hamas ke garkuwa da su

Isra’ila ta kai sabbin hare-hare yankin Zirn Gaza a Lahadin nan a yayin da mahukuntanta ke shan matsin lamba a kan ceto karin mutanen da har yanzu Hamas  ke  garkuwa da su sama da watanni biyu da suka wuce, tun bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba.

Fira ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu.
Fira ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu. AP - Ronen Zvulun
Talla

Firaminisa Minister Benjamin Netanyahu ya fuskanci zanga-zanga a ranar Asabar daga ‘yan uwan wadanda Hamas ta ke garkuwa da su, inda suke kira a sake cimma wata karin yarjejeniyar tsagaita wuta don karbo mutanensu.

Hamas ta ce martanin da Isra’ila ke mayarwa dangane da harin 7 ga watan Oktoba da ta kai cikin kasarta ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 18 da dari 8 ya zuwa yanzu.

A  yayin wata  zanga-zanga a birnin Tel Aviv a ranar Asabar, ‘yan uwan mutanen da ake garkuwa da su sun yi magiya ga gwamnatin Isra’ila don cimma yarjejeniyar da za ta kai ga sakin ‘yann uwansu.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu  ya  yi wasu kalamai a ke nuna cewa za a sake wata yarjejeniyar tsagaita wuta don sakin wadanda Hamas ke garkuwa da su nan ba da jimawa ba.

A wani taron manema labarai da aka watsa ta tashar talabijjin kasar, Netanyahu ya bayyana yakin da kasarsa ke yi da Hamas a matsayin yakin tabbatar da wanzuwa a matsayin al’umma, wanda dole sai an yi nasara, duk kuwa da matsin lamba da kuma asarar da ake tabkawa.

Wadannan kalamai nasa na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar sojin kasar ta ce dakarunta sun kashe wasu wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza bisa kuskure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.