Isa ga babban shafi

Kungiyar Yahudawa a Amurka ta yi zanga-zangar neman tsagaita wuta a Gaza

Wata kungiyar yahudawa da ta bukaci Israila ta tsagaita wuta a zirrin Gaza, ta gudanar da zanga zanga a birane 8 ta Kasar Amurka, inda ta hadda cunkoson ababen hawa a kan hanyoyi da gadaje dake biranen Washington da Philadelphia.

Yadda wasu yankunan Gaza suka lalace sakamakon hare-haren Isra'ila.
Yadda wasu yankunan Gaza suka lalace sakamakon hare-haren Isra'ila. AP - John Minchillo
Talla

 

Biranen da aka gudanar da wannan zanga zanga dai sun hada da Boston, da Atlanta, da Chicago, da Minneapolis, da Seattle da Portland da kuma Oregon.

A birnin Philadelphia, akalla masu zanga zanga 200 ne suka tare babbar hanyar matafiya cikin gajeren lokaci, rike da allunan dake dauke da rubutun dake cewa, ‘’ku bar Gaza ta rayu,’’ kazalika sama da mutane 30 da suka yi ba daidai ba aka kama a wannan tattakin.

Rundunar ‘yan sandan Amurka ta ce yayin zanga zangar da mambobin kungiyar yahudawan 90 suka gudanar dan neman tsagaita wuta a zirrin Gaza, sun kuma toshe hanyar da ta kasance mahadin birnin newyork da  yankin arewa maso yammacin babban birnin Kasar, dalilin da ya sa shawartar mutane su yi amfani da wasu hanyoyi na daban.

Kungiyar ta sanar a shafinta na X da aka fi sani da Twitter batun gagarumar taron da suke gudanarwa a dare na 8 na bikin Hanukkah a cikin birane 8, kuma a kan gadoji 8 dake Kasar, ta ce adadin masu zanga zangar na cigaba da karuwa dan neman dakatar da rikicin.

A ranar talata da ta gabata ne majalisar dinkin duniya ta bukaci gaggauta tsagaita wuta a zirrin Gazar da israila ta sha alwashin cigaba da barin wuta har sai ta ga bayan mayakan Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.