Isa ga babban shafi

Isra'ila ta ce ta yi kuskuren kashe wasu da aka yi garkuwa da su a Gaza

Wasu mutane 3 da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza sun gamu da  ajalinsu bayan da sojojin Isra’ila suka harbe su bisa kuskure, kamar yadda rundunar sojin kasar ta bayyana a wata sanarwa, a Juma’a.

Um soldado israelense se posiciona em um local indicado como Gaza, em meio à operação terrestre em andamento do exército israelense contra o grupo islâmico palestino Hamas, nesta imagem divulgada em 2
Wani soojin Isra'ila a Zirin Gaza. via REUTERS - ISRAEL DEFENSE FORCES
Talla

Rundunar sojin Isra’ila ta ce lamarin ya auku ne a yayin da ake bata kashi a yankin  Shejaiya mai cinkoson jama’a a birnin Gaza, inda bisa kuskure dakarun suka dauka mutanen na da hatsari a gare su, kuma suka bude musu wuta.

Sojin Isra’ila ta ce wadanda aka kashe bisa kuskuren sune, Samer Talalka da Yotam Haim, wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da mayakanta suka kai hari cikin Isra’ila. Daga bisani ta kuma bayyana sunan mutum na uku da aka kashe mai  suna Alon Shamriz.

Tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba ne sojinkasar suke ta yin luguden wuta a yankin Falasdinawa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dimbim mutane a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe na ta kiraye-kirayen tsagaita wuta don kawo karshen mace=mace, amma Isra’ila ta yi biris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.