Isa ga babban shafi

Hamas ta shiga neman wasu 'yan kasar Rasha 8 da aka yi garkuwa da su a Gaza

Wani babban jami'in kungiyar Hamas Moussa Abou Marzouk da ke ziyara a birnin Moscow ya bayyana a jiya Asabar cewa kungiyar Hamas tana kokarin tantance wurin da wasu mutane takwas 'yan Rasha dake da takardar Isra'ila da aka yi garkuwa da su  a Gaza domin kubutar da su.

Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh
Shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh REUTERS - AZIZ TAHER
Talla

Kamfanin dillancin labaran Rasha ya ruwaito cewa jami'in ya ce "Yanzu muna neman mutanen da bangaren Rasha ya bayar da rahoto, abu ne mai wahala, amma muna neman su. Kuma da zarar mun same su, za mu sake su."

 Jami’in ya bayyana cewa, ya samu bayyanai daga ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha tareda samun jerin sunayen mutane biyu na Rasha.

Moussa Abou Marzouk ya ce "Muna mai da hankali sosai kan wannan jerin sunayen kuma za mu kula da su saboda muna daukar Rasha a matsayin aminiyarmu ta kud da kud."

Shugaban Rasha yayin ganawa da yan kungiyar Hamas a Rasha
Shugaban Rasha yayin ganawa da yan kungiyar Hamas a Rasha via REUTERS - SPUTNIK

 

Shugaban Hamas ya isa birnin Moscow a ranar Alhamis domin tattaunawa, wanda shi ne na farko tun vayan barkewar rikicin tsakanin Isra'ila  da Hamas  kusan makonni uku da suka gabata.

Wadannan shawarwarin sun hada da sakin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su da kuma kwashe 'yan kasar Rasha.

A ranar Talata, fadar Kremlin ta yi nuni da cewa, babu wani ci gaba da aka samu wajen kubutar da 'yan kasar Rasha da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a harin da aka kai a ranar 7 ga watan Oktoba a Isra'ila, har ma ta amince da cewa ba ta san adadinsu ba. Hamas ta yi garkuwa da kusan mutane 230, Isra’ilawa, ‘yan kasashen waje ko ‘yan kasashen biyu, a cewar Isra’ila.

Yakin Isra'ila da Hamas
Yakin Isra'ila da Hamas © Ariel Schalit / AP

Daruruwan ‘yan kasar Rasha ne kuma ke zaune a zirin Gaza, inda hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke kaiwa a matsayin ramuwar gayya ga harin Hamas.

Shi kuwa Moussa Abou Marzouk ya yi nuni da cewa, babu wani ci gaba a tattaunawar da ake yi na kubutar da sauran mutanen Hamas da aka yi garkuwa da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.