Isa ga babban shafi

Karin motoci 17 dauke da kayan agaji sun shiga Zirin Gaza ta mashigin Rafaa

Manyan motocin dakon kaya 17 dauke da kayan agaji sun isa Zirin Gaza da safiyar yau Litinin, yayin da aka shiga rana ta biyu da Isra’ila ta bayar da damar shigar da kayan agaji yankin da take ci gaba da yiwa ruwan wuta.

Yadda motoci ke shiga Gaza ta mashigin Rafa
Yadda motoci ke shiga Gaza ta mashigin Rafa REUTERS - STRINGER
Talla

Kamfanin dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa motocin sun isa yankin ne daga Masar dauke da kayan don ci gaba da taimakawa jama’ar da rikicin ya rutsa da su.

Bayanai na nuna cewa mafi yawan kayan da motocin suka dauko kayan abinci ne da magunguna, wadanda za’a yi amfani da su a asibitoci don ceto rayukan mutanen da suka jikkata, a sanadin hare-haren Isra’ila.

Tun a jiya Lahadi ne dai motoci 20 suka dauki hanyar su ta isa Zirin Gazar makare da kayayyakin agaji.

Kididdigar majalisar dinkin duniya ta nuna cewa wannan kaya da suka shiga yankin, bai wuce kaso 4 cikin 100 na adadin abinda ke shiga yankin kowacce rana ba, kafin a fara yakin, tana mai cewa shigar motoci 100 na kayan agaji kowacce rana shine zai ishi mutane miliyan 2 da dubu dari 4 da ke rayuwa a yankin da ke zaman guda cikin yankuna mafi cinkoso a duniya.

Kananan yara da mata sune suka fi tsananin bukatar wadannan kayayyaki la’akari da yadda hare-haren suka fi shafar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.