Isa ga babban shafi

Kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi tir da hare-haren Isra'ila a Gaza

Gamayyar kungiyoyin fararen hula da suka hada da na Kwadago, masu kare hakkin dan Adam, kungiyoyin dalibai da sauran daidaikun masu ruwa da tsaki a Najeriya, sun yi  Allah wadai da hare-haren da Isra’illa ke kai wa kan fararen hula a Zirin Gaza. 

Wasu da harin Isra'ila ya rustsa da su a yankin Gaza.15/10/23
Wasu da harin Isra'ila ya rustsa da su a yankin Gaza.15/10/23 REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

Taron gamayyar kungiyoyin fararen hular na Najeriya da ya gudana a birnin Legas, ya aike da jerin sakwannin jan hankalin ga Isra’ila da sauran kasashen duniya, wadanda suka ce sun cimma matsaya akansu bayan nazartar halin da ake ciki a Gaza. 

Allah wadai da hare-haren Isra'ila

Sako na farko dai shi ne amfani da kakkausan harshe wajen yin Allah wadai da hare-haren kare dangin da Isra’ila ke kaiwa fararen hular da suka hada da mata da kananan yara, yayin da adadin wadanda ke mutuwa daga cikinsu ke karuwa. 

Kungiyoyin farar hular sun kuma bayyana harin Isra’ila da ya kashe mutane sama da 500 a asibitin Al Ahli baptist da ke gaza a matsayin laifin yaki, yayin da suka bayyana Fira Minista Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Joe Biden a matsayin wadanda suka hada gwiwa wajen aikata mummunan laifukan yaki, baya ga yunkurin karyar cewa Isra’ila ba ta da hannu a harin da aka kaiwa asibitin na Gaza. 

Masu fafutukar sun kuma bayyana farmakin da mayakan Hamas suka kaiwa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, a matsayin ramuwa kan azabar da gwamnatin Isra’ila ta shafe sama da shekaru 70 tana gana wa Falasdinawa, tashin hankalin da suka ce al’ummar Afirka sun fuskanci makamancinsa a zamanin mulkin mallakar da turawa suka yi wa kasashen nahiyar. 

Jinjina ga zanga-zangar Yahudawa

Wani batu da gamayyar kungiyoyin farar hular na Najeriya suka yi tsokaci akai shine jinjinawa daruruwan Yahudawa mazauna Amurka suka yi zanga-zanga a gaban fadar White House don yin tir da kisan kare dangin da take yi wa Falasdinawa a Gaza. 

‘Yan fafutukar na Najeriya da suka bukaci kasashen Larabbawa da Turkiya da China su kawo karshen kaka gidan da Amurka ke yi wa a sassan duniya, sun kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta kori jakadan Isra’illa daga kasar saboda laifukan yakin da kasarsa ke aikata wa, ta kuma dakatar da duk Hulda da Isra’ila har sai Falasdinawa sun samu ‘yanci. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.