Isa ga babban shafi

Shugaban kasar Iran ya ziyarci China domin karfafa dangantaka

Kafar yada labaran kasar Iran ta bayyana cewa shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi zai kai ziyarar kwanaki uku a kasar China da nufin karfafa alaka da babbar abokiyar cinikayyar kasar Iran.

Shugaban kasar Iran  Ebrahim Raïssi
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raïssi via REUTERS - OFFICIAL PRESIDENTIAL WEBSITE
Talla

Ibrahim Raisi zai bar Tehran da yammacin gobe litinin zuwa birnin Beijing, bisa gayyatar takwaransa Xi Jinping, kamar yadda hukumar ta Iran ta bayyana.

Shugabannin biyu sun fara ganawa ne a watan Satumba a taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan.

A yayin wannan taro, shugaban na Iran ya yi kira da a karfafa dangantakar tattalin arziki da birnin Beijing, musamman a fannonin "man fetur da makamashi, zirga-zirgar jiragen sama, noma, kasuwanci da zuba jari".

A watan Maris din shekarar 2021, Iran ta cimma yarjejeniyar hadin gwiwa ta dabaru da kasuwanci na tsawon shekaru 25 da kasar China, “abokiyar lokutan gwaji”, bayan shafe shekaru ana tattaunawa.

Kasar China ita ce babbar abokiyar cinikayyar Iran, in ji Iran bisa kididdigar da aka yi. Kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa China ya kai dala biliyan 12.6 kuma ta shigo da dala biliyan 12.7 a cikin watanni goma na farkon shekarar Iran wanda ya fara a watan Maris na 2022.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.