Isa ga babban shafi

Iran na bikin zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci

Dubban mutane a Iran na bikin cikar kasar shekaru 44 da zama jamhuriyar musulunci, abinda ke zuwa yayin da masu zanga-zanga suka shafe tsahon watanni suna zanga-zangar a titunan kasar.

Tutocin kasar Iran
Tutocin kasar Iran REUTERS/Morteza Nikoubazl
Talla

Ba kamar shekaru biyu da suka gabata ba, inda aka gudanar da bikin a cikin motoci saboda cutar Corona, a bana jama’a ne suka kwarara kan tituna suna tafiya a kafa yayin da suke rungumar juna da taya juna murnar zagayowar ranar.

Wasu faya-fayan bidiyo da suka rika yawo sun nuna yadda jama’a ke daga tutocin kasar suna kuma rera wakokin da ke tir da manufofin kasashen turawa game da addinin musulunci da kuma Saudiyya wadda akidar su ta sha bam-bam.

Bayanai sun ce an zagaye babban filin taro da ke tsakiyar kasar da na’urorin tarwatsa makami mai linzami da kananan jirage marasa matuka guda 136 dake shawagi don hango wata barazana daga nesa kafin Isar shugaban kasar Ebrahim Raizi da za iyi jawabi.

Bikin dai na tunawa da ranar faduwar gwamnatin Shah da ya zo kwanaki 10 bayan komawar fitacce malami Shi’a Ali Khomeini daga gudun hijirar da yayi a watan Fabrairun 1979

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.