Isa ga babban shafi

Mutane 9 sun mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai kusa da Damascus

Wani hari da Isra'ila ta kai a kusa da birnin Damascus na Syria a ranar Laraba ya kashe mayaka tara, cikinsu har da sojojin Syria biyar.

Jiragen yakin Isra'ila.
Jiragen yakin Isra'ila. © US Air Force/Senior Airman Jerreht Harris
Talla

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria ta ce wani wurin ajiyar harsasai da wasu wurare da ke da alaka da kasancewar sojojin Iran a Syria na daga cikin wadanda Isra’ila ta kaiwa farmaki.

Kafofin yada labaran gwamnati a Syria sun tabbatar da hudu daga cikin biyar da suka mutu a hare-haren, yayinda Isra'ila ta ki cewa komai akai.

Wasu alkaluma da masu bibiyar lamurran yankin Gabas ta Tsakiya suka tattara sun nuna cewar Isra'ila ta kai daruruwan hare-hare a kan wasu yankuna a Syria tsawon shekaru, said ai ba ta faye yin Magana akan su ba.

Sai dai Isra’ilar ta sha bayyana cewar tana kai hari ne kan sansanonin mayakan sa-kai da ke kawance da Iran, kamar kungiyar Hizbullah ta Lebanon, wadda ke da mayaka a Syria masu marawa gwamnatin Bashar al-Assad baya. Kuma tana kokari ne wajen dakile jigila ko safarar makaman da ake kyautata zaton na mayakan sa kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.