Isa ga babban shafi
sYRIA - isra'ila

Isra'ila ta harba makamai masu linzami sansanin sojin saman Syria

Hare-haren sama da Isra’ila ta kai kan sansanin sojin sama da ke tsakiyar Siriya ya raunata sojoji Syria shida da barnata dukiyoyi, kamar yadda kafafen yada labarai na gwamnati suka ruwaito.

آسمان دمشق، بعد از حملات اسرائیل
آسمان دمشق، بعد از حملات اسرائیل © AFP
Talla

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya ce "Da misalin karfe 9 na daren Jumma’a Isra'ila ta harba makamai masu linzami  kan sansanin sojin sama na T4 da ke lardin Homs.

Kungiyar dake sa’ido a rikicin kasar Syria tace jiragen saman yakin Isra’ila ne suka kai hari kan wani wurin ajiye jirage marasa matuka a filin jiragen sama da ke tsakiyar Syria.

Kamfanin dillancin labarai na SANA wanda baiyi cikakken ƙarin bayani ba yace "dakarun tsaron sararin samaniyar Syria sun kakkabo makami mai linzami a sararin samaniyar Homs."

Shugaban kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria, da ke da cibiya a Burtaniya, Rami Abdul Rahman, yace ba’a samu rasa rayuka ba.

Tun bayan barkewar yakin basasar Syria a shekarar 2011, Isra’ila ta saba kai hare -hare a cikin Syria, galibi tana kaiwa sojojin Hizbullah na Iran da Lebanon da kuma sojojin gwamnatin Syria hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.