Isa ga babban shafi

Mayakan Houthi sun yi wa Saudiya tayin sulhu

Yan tawayen Huthi na kasar Yemen sun gabatar da tayin tsagaita wuta da tattaunawar zaman lafiya domin kawo karshen yakin da suka shafe shekaru kusan 7 suna gwabzawa da sojojin kawancen da Saudiya ke jagoranta.

Wani yankin birnin Sana'a na kasar Yemen, da yakin Saudiya da 'yan tawayen Houthi ya ragargaza.
Wani yankin birnin Sana'a na kasar Yemen, da yakin Saudiya da 'yan tawayen Houthi ya ragargaza. AP - Hani Mohammed
Talla

Cikin tayin da suka gabatar, mayakan na Houthi sun yi alkawarin bude filin tashi da saukar jiragen sama na babban birnin Yemen, wato Sana’a, da kuma babbar tashar jiragen ruwa ta Hodeida, kamar yadda wani babban jami’in Saudiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a yau Asabar.

Bukatar ‘yan Houthin na zuwa ne kwana guda bayan hare-haren da suka kaiwa sassan Saudiya da makamai masu linzami, ciki har da wata cibiyar mai a birnin Jeddah, lamarin da ya haifar da mummunar gobara da ta haifar da fargaba a tsakanin masu halartar gasar tseren motoci na Formula One.

A makon jiya ne dai ‘yan tawayen da Iran ke marawa baya suka yi watsi da tayin tattaunawar sulhu a Riyadh babban birnin Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.