Isa ga babban shafi
Saudiya - Huthi

Saudiya ta sanar da rage man da take hakowa bayan harin Huthi

Kasar Saudiyya dake ja gaba a harkar fitar da gangan danyen mai a duniya ta sanar da rage yawan man da take hakowa na wani dan lokaci a wata cibiyar da ke karkashin kamfanin makamashi na Aramco, bayan da 'yan tawayen Huthi na Yaman suka kaddamar da hare-haren da dama.

Wata cibiyar sarrafa man Saudiya ta ARAMCO
Wata cibiyar sarrafa man Saudiya ta ARAMCO AP - Amr Nabil
Talla

Ma'aikatar makamashin Saudiya cikin wata sanarwa tace an dan rage aikin ne bayan wani harin da jirgin sama mara matuki kan matatar mai na YASREF da ke birnin Yanbu mai masana'antu da ke kan tekun Red Sea, wanda bai haifar da  asarar rai ba.

Sanarwar ta ruwaito wani jami’in ma’aikatar yana cewa, an kaddamar da hare-haren da jirage marasa matuka har sau biyu da misalin karfe 5:30 na safe agogon kasar a tashar iskar gas ta Yanbu da kuma wani a kamfanin YASREF mai samar da ganga dubu 400.

Jami'in ya yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai cewa sun biyo bayan harin da aka kai ranar Asabar a tashar rarraba albarkatun man fetur da ke Jizan a kudancin kasar.

'Yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran, wadanda ka adawa da Saudiyya dake jagorantar kawancen soji a Yemen, sun sha kai hari kan masarautar, ciki har da wuraren da Aramco ke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.