Isa ga babban shafi
Yemen -Saudiyya

'Yan tawayen Houthi sun kai hare-hare matatun man Saudiyya

Mayakan ‘yan tawayen Houthi a kasar Yemen sun ce sun kai hare hare da jirtage marasa matuki har 14 a biranen Saudiyya da dama a jiya Asabar, ciki har da  cibiyoyin kamfanin main a Aramco da ke birnin Jeddah, a yayin da kuma kamfanin dillancin labaran Saudiyya ke cewa hadakar da ke karkashin jagorancin kasar ta kaddamar da hare hare a sansanoni 13 na ‘yan Houthi a Yemen.

'Yan tawayen Houthi sun baje kolin jirage marasa matuki.
'Yan tawayen Houthi sun baje kolin jirage marasa matuki. - AL-HUTHI GROUP MEDIA OFFCIE/AFP/File
Talla

A wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, kakakin mayakan Houthi Yahya Saree, ya ce lallai sun kai hari kan matatun man kamfanin Aramco a Jeddah, da ma wasu cibiyoyin soji a Riyadh, Jeddah, Abha, Jizan da Najran.

Saree ya ce hare haren martani ne ga dirar mikiya da hadakar dakaru, karkashin jagorancin Saudiyya ke ci gaba da yi wa Houthi, da kuma mamayar da ta yi wa Yemen.

Babu karin bayani daga hadakar dakarun da ke karkashin Saudiyya a kan wannan ikirari na mayakan Houthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.