'Yan Houthi sun zartas da hukuncin kisa kan mutane 9 da suka kashe jagoran su
'Yan tawayen Huthi da ke Yemen zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane 9 a yau Asabar, wadanda suka samu da hannu a kisan daya daga cikin manyan shugabanninsu, yayin wani hari ta sama da Saudiyya ta jagoranta a shekarar 2018.
Wallafawa ranar:
Kafin mutuwar sa Saleh al-Sammad shi ne shugaban majalisar kolin Siyasar Houthi, wanda rashin sa ya zamewa 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Iran koma baya.
Mutanen 9 da ‘yan tawayen na Houthi suka harbe, na cikin 16 da kotun su ta samu da hannu a kisan jagoran na su.aaa
Daga cikin sauran mutane 7 da aka yankewa hukuncin kisan duk da basa nan kuma akwai Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
An kashe Sammad a watan Afrilun shekarar 2018 tare da wasu mutane shida a wani hari ta sama a lardin Hodeida da ke Yemen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu