Isa ga babban shafi
Yemen

Hare-haren Huthi ya hallaka sojojin gwamnati 30 a Yemen

An kashe akalla dakarun gwamnatin Yemen 30 a wani farmaki da aka kaddamar kan sansaninsu mafi girma a kasar, yayin da aka zargi mayakan Huthi da hannu a harin na karshen mako.

'Yan tawayen Houthi dake Yamen cikin mota 16/02/21.
'Yan tawayen Houthi dake Yamen cikin mota 16/02/21. AP - Hani Mohammed
Talla

An kai harin ne a sansanin Al-Anad na sojin saman Yemen mai tazarar kilomita 60 daga birnin Aden, birnin  na biyu mafi girma a kasar mai fama da yake-yake.

Wannan sansanin sojin saman na Al-Anad a can baya,  ya taba kasancewa shalkwatan dakarun Amurka da suka  sanya ido kan hare-haren jirage marasa matuka da aka kai kan mayakan Al-Qaeda har zuwa shekarar 2015, wato gabanin mayakan Huthi su karbe iko da yankin.

Mai magna yawaun sojojin sama na Yemen, Mohammed Al-Naqib ya tabbatar da harin na ranar Lahadi, inda har ya ce, akwai karin dakaru 56 da suka jikkata.

Jami’in ya kara da cewa, mayakan Huthi masu bin akidar Shi’a, sun cilla makamai masu linzami kan sansanin, sannan suka yi amfani da kurman jirgin yaki a farmakin.

Tuni shugaban Yemen Abedrabbo Mansur Hadi ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan mamatan da lamarin ya rutsa da su, yana mai shan alwashin daukar fansa kan mayakan .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.